Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: 'Yancin Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AP

Yankin kudancin Sudan zai samu 'yancin kai, inda zai zama jamhuriyar Sudan ta Kudu, shekaru shidda daidai tun bayan soma aiwatar da yarjajeniyar kawo zaman lafiya tsakanin bangarorin Sudan da ke yaki.

Kimanin kashi 99 ne cikin dari na al'ummar yankin, suka kada kuri'ar raba-gari da yankin arewa, a kuri'ar raba-gardamar da aka gudanar a watan Janairun da ya wuce.

Sassan biyu dai sun kwashe fiye da shekaru ashirin suna yakin basasa, wanda kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane kimanin miliyan biyu.

Yankin kudancin Sudan dai yanki ne mai dazuzuka da koramu, yayin da yankin arewa kuma yanki ne mai hamada.

Yawancin mazauna arewacin Sudan Musulmi ne, masu amfani da harshen Larabci, yayin da su kuma 'yan Kudu sun fito ne daga kabilu dabam-dabam, wadanda galibi Krista ne, ko kuma masu bin addinan gargajiya.

'Yan kudancin Sudan da yawa na kokawa da wariyar da suka ce gwamnatin arewacin kasar na nuna masu, kuma sun fusata da yunkurin da gwamnatin ke yi na kafa shari'ar Musulunci a dukan fadin kasar.

Shugaban arewacin Sudan din, Omar al Bashir, ya ce shi ma zai halarci bukukuwan da za a yi a Juba, babban birnin yankin.

To bayan bikin, sai kuma me? Wane kalubale ne arewaci da kudancin Sudan din za su fuskanta bayan kowane ya kama gabansa?

To bakin da muka gayyato domin tattaunawa a kan wadannan batutuwan sun hada da Ambasada Dahiru, tsohon jakadan Najeriya a Sudan da Farfesa Saleh Dauda, na sashen nazarin ilimin siyasa a jami'ar Abuja da kuma Salmanu Parisi, wani dan jaridar Sudan, wanda yanzu haka yake birnin Juba na kudancin Sudan.

Akwai kuma masu sauraro da yawa akan layi. Ayi sauraro lafiya.