Ra'ayi Riga: Zargin kisan gilla da fyade a Maiduguri

Jami'an 'yan sanda a Maiduguri
Bayanan hoto,

Jami'an 'yan sanda a Maiduguri

Hare-haren da kungiyar Ahlus-Sunna Lid-da'awati wal Jihad ko Boko Haram ke kaiwa a wasu sassan arewacin Najeriya na dada karuwa da zafafa.

Ko a watan da ya wuce kungiyar ta kai mummunan hari a hedkwatar 'yan sandan Najeriyar a Abuja, inda aka sami hasarar rayuka da dukiya mai dimbin yawa.

Sai dai lamarin ya fi kamari ne a Maiduguri, babban birnin jahar Borno, inda kusan a kowace rana a baya bayan nan ake kai hare-haren bam da kuma yin musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar ta Ahlus-Sunna Lid-da'awati wal jihad wadda aka fi sani da Boko Haram.

Mutane da yawa na rasa rayukansu ko jikkata, kuma a yanzu haka jama'a na ta kaura daga birnin na Maiduguri.

A kokarin magance matsalar ne aka tura rundunar hadin gwiwa ta JTF.

Sai dai jama'ar Maidugurin na kokawa da jami'an tsaron, wadanda suke zargi da aikata kisan gilla, da yin fyade, da satar dukiyar jama'a da dai sauransu.

Zargin da Jami'an tsaron ke musantawa, inda su kuma suke zargin jama'ar Maidugurin da kin ba su hadin kai wajen gano inda 'yan kungiyar su ke.