Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Shekaru 10 bayan harin 9/11

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hare-haren sun sauya al'amura a duniya

A ranar Lahadi ne ake cika shekaru goma cir-cir da hare-haren da aka kai a Amurka. Lamarin da ya sauya yadda al'amura ke gudana a duniya baki daya.

Daruruwan mutane ne, Amirkawa da sauran 'yan kasashen waje suka rasa rayukansu.

Nan da nan ne kuma Amurka ta dora alhakin hare-haren a kan kungiyar masu fafutukar Islama ta al-Qaeda. Da farko dai al-Qaedar, a karkashin jagorancin Osama bin Laden, ta musanta zargin, kamin daga baya ta dauki alhakin kai hare-haren, a shekara ta 2004.

Ta ce ta yi hakan ne saboda irin goyon bayan da Amurka ke baiwa Isra'ila, da kuma kasancewar sojan Amurka a Saudiyya, tare da takunkumin da aka sa wa Iraki.

Hare-haren dai sun sa Amirka, tare da wasu kawayenta sun kaddamar da yaki a kan ta'addanci.

Sun mamaye Afghanistan inda suka kawar da gwamnatin Taliban, wadda suka zarga da bayar da mafaka ga 'yan kungiyar al Qaeda.

Domin tattaunawa kan wannan batu, mun gayyato Dr. Abubakar Dan Lami Alhassan, malami a sashen koyar da aikin jarida a jami'ar Bayero da ke Kano, wanda yana Amurka lokacin da abin ya faru.

Akwai kuma Kwamishinan 'yan sandan jahar Rivers a Najeriya, Alhaji Sulaiman Abba, da Hon. Rabe Nasir, tsohon shugaban kwamitin yaki da ta'addanci a majalisar wakilan Najeriya.

Dokta Aliyu Tilde, mai sharhi kan al'amura a Najeriya da Malam Musa Aliyu na cibiyar nazari kan yaki da samar da zaman lafiya ta Desmond Tutu, a birnin Liverpool na nan Ingila.

Sai kuam Injiniya Yusuf Abdulkarim Iyimoga a Kabul, babban birnin Afghanistan.