Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Tashe-tashen hankula a Jos

Image caption Rikicin ya haifar da hasarar rayuka da dukiyoyi da dama

Yau kusan shekaru goma kenan da ake fama da rikice-rikice a jihar Pilato dake Tsakiyar Najeriya.

Rikice-rikicen, wadanda keda nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa, sun ci gaba da haddasa asarar rayuka da dukiya masu yawan gaske.

Gwamnatin Tarayya dai ta sha kafa kwamitocin bincike a kan rikice-rikicen, wadanda suka bada shawarwari kan yadda za a magance su, sannan gwamnatin Tarayyar ta girke runduna ta musamman STF don tabbatar da tsaro a jihar, amma ga alama har yanzu rikicin ya ki ci ya ki cinyewa.

Sai dai a cikin wannan makon, shugaba Goodluck Jonathan ya umarci Babban hafsan tsaron kasar, Air Marshal Oluseyi Petinrin, da ya karbi baki dayan aikin kula da harkokin tsaro a jihar ta Pilato, a wani yunkuri na kawo karshen rikicin da jihar ke fama da shi.

Galibin al'ummomin jihar ta Pilato dai sun yi marhabin da wannan mataki.

Sai dai tambaya a nan ita ce ko wannan mataki shi kadai ya isa ya maido da zaman lafiya a jihar ta Pilato? Me ya kamata a yi don samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar?

To domin tattauna wannan batu, mun gayyato wasu baki wadanda suka hada da :

Mr Abraham Yiljap, Kwamishinan yada labaran jihar Pilato da Ambassada Yahaya Kwande, wanda ke jagorantar kwamitin da shugaba Jonathan ya kafa, tare da Cif Solomon Lar .

Akwai kuma Dr Jonah Madugu, wakilin 'yan kabilar Berom da Alhaji Sani Mudi, wakilin Hausawa, kuma Sakataren Majalisar malamai ta jihar Pilato

A kwai kuma Rev. Philips Mweldish Dafes, shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN, reshen jihar Pilato.