Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Batun sabon tsarin albashi a Najeriya

Image caption 'Yan kwadagon Najeriya na zanga-zanga a jihar Enugu

A Najeriya a farkon bana ne shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya rattaba hannu akan dokar da kayyade albashi mafi karanci a kasar na Naira dubu goma sha takwas a wata.

Yayin da tuni wasu jihohin kasar suka amince su aiwatar da wannan sabon tsarin albashin.

Da alama batun na neman jikawa wasu jihohi aiki don kuwa sun ce ba za su iya biya ba abin da ya kaiga yajin aiki a jihohin.

A wasu jihohin kuma, ma'aikatan sunce suna jira ne wa'adin da gwamnati ta dibar masu na biyan sabon tsarin albashin ya kare sannan su san matakin da za su dauka

Ta yaya za'a warware wannan matsalar biyan sabun tsarin albashin ma'aikata dake neman gurgunta ayyukan gwamnati a wasu jahohin Nigeria?

To don tattaunawa akan wannan batu a mun gayyato Comrade Ayuba Waba, ma'ajin kungiyar kwadago ta kasa, kuma shugaban kungiyar likitoci da ma'akatan jinya ta Nigeria.

Akwai kuma Owelle Rochas Okorocha gwamnan Jihar Imo, daya daga cikin jihohin da ma'ikata ke yajin aiki akan maganar albashin.

Muna kuma tare da Bashir Gambo Saulawa, mashawarci na musanman ga gwamnan jihar Katsina akan harkokin kwadago, wanda shi ma yake tareda mu tawaya daga Katsina, inda acanma yajin aikin akeyi.

Akwai kuma Bashir Hayatu Jantile, wani dan siyasa a Najeriya kuma mai sharhi akan al'amurran yau da kullum, wanda ke dakinmu na hada shirye-shirye a London.