Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Faduwar jarabawar sakandare a Najeriya

Image caption Ana danganta faduwar yaran da abubuwa da dama

A Najeriya a 'yan shekarun da suka wuce dai, sakamakon jarabawar kammala karatun sakandare watau SSCE, ya yi munin gaske inda galibin yaran da ke rubuta jarabawar ke faduwa warwas.

Bana ma dai, ba ta sauya zane ba, inda kamar yadda Hukumar da ke shirya jarabawar, NECO ta yi bayani, kasa da kashi 25 kacal cikin 100 ne na yara miliyan daya da dubu dari da sittin da wani abu da suka rubuta jarabawar, suka yi nasara.

Hakazalika, Hukumar ta NECO ta ce yaran sun fadi sosai a Lissafi da Turanci inda kashi 23 daga cikin 100 ne kawai suka yi nasara a Turanci, sannan kashi 25 cikin 100 ne kawai na yaran suka yi nasara a Lissafi.

Hakanan kuma Hukumar ta NECO ta ce an yi ciwa-ciwa fiye da dubu dari 4 a lokacin jarabawar ta SSCE.

To shin wai wadanne dalilai ne suka sa aka samu irin wannan yanayi na faduwar jarabawar karshe ta kammala sakandare a Najeriya? Me kuma ya kamata a yi don a daidaita al'ammura?

To domin tattaunawa akan wannan batu mun gayyato wasu baki da suka hada da:

Farfesa Ahmed Modibbo, Babban Sakataren Hukumar samar da Ilimin firamare ga kowa, UBEC, da Barrister Faruk Iya, Kwamihsinan Ilimi na jihar Kano.

Akwai kuma Alhaji Huseini Zakari, kakakin kungiyar malaman makaranta ta NUT da Alhaji Adamu Aliyu Kiyawa, mai makarantar Gateway International School da ke Kano.

Sai kuma Dr Aliyu Tilde, mai sharhi kan al'ammuran yau da kullum a Najeriya,wanda kuma yanzu haka yake Ofishinmu na Abuja ...

Mun kuma gayyaci Hukumar NECO don shiga shirin, amma shugabanta, Farfesa Promise Okpala, wanda ke Filin jirgin saman Abuja a lokacin da muka yi magana da shi, wanda ya ce an sanar da shi ne a kurarren lokaci, saboda haka ba zai iya shiga shirin, ko ya wakilta wani daga cikin ma'aikatansa, don gudun fadin wani abin da ba shi ba ne.