Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Yawan jama'a na barazana ga duniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yawan jama'ar duniya zai kai biliyan bakwai

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a cikin wannan makon, ya nuna cewa a ranar 31 ga wannan watan na Oktoba ne, yawan al'ummar duniya zai kai biliyan bakwai.

Duk da cewa za a samu raguwar haihuwa a wasu kasashen duniya, rahoton ya yi hasashen cewa yawan al'ummar duniya zai ci gaba da karuwa, inda zai kai biliyan takwas a shekara ta 2025, har ma ya zarta biliyan goma a karshen wannan karni.

Majalisar Dinkin Duniya dai tana nuna damuwa cewa karuwar yawan al'umma cikin sauri a kasashe matalauta da dama, za ta iya haddasa cibayan kasashen, abun da zai sa al'ummominsu cikin kangin tallauci da yunwa.

To ko wane irin kalubale ne za a fuskanta a sakamakon yawan karuwar al'ummar?

Wane irin tanadi ne ya kamata gwamnatoci su yi domin fuskantar kalubalen da kuma kyautata zamantakewar al'umma?

Kadan kenan daga cikin irin abubuwan da za mu tattauna a kai a cikin Filinmu na Ra'ayi Riga.

To domin tattauna wannan batu mun gayyato wasu baki da suka hada da: Mr Jamin Dora Zubema, Direkta Janar na Hukumar kula da al'umma ta Najeriya, NPC, wanda yanzu haka yake Ofishinmu na Abuja.

Akwai kuma Dr Yusuf Adamu, malami a jami'ar Bayero da ke Kano da Malam Dauda Tankama, mataimakin shugaban kawancen kungiyoyin farar hula na CADDED a Jumhuriyar Nijar..

Sai kuma Malam Alhassan Abdullahi, shugaban kungiyar EANFORWORLD mai fafutukar kare muhalli a Ghana.