Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matsalar ciwon sukari

Hakkin mallakar hoto AFP

Alkalumman da Hukumar Lafiya ta Duniya ta wallafa sun nuna cewa, kusan mutane miliyan dari ukku da hamsin ne a duniya ke fama da ciwon suga, ko kuma diabetes. kuma mafi yawan mace macen da ake samu, sakamakon ciwon sugar, suna faruwa ne a kasashe masu tasowa.

A hasashen da ta yi, hukumar lafiyar ta ce idan ba mataki aka dauka ba, to kuwa adadin mutanen da za su mutu sakamakon kamuwa da cutar zai ninka har sau biyu, tsakanin shekara ta dubu biyu da biyar zuwa dubu biyu da talatin.

Don haka ne ma a wannan shekarar, albarkacin bukukuwan da ake yi a kowace ranar goma sha hudu ga watan Nuwamba, domin tunawa da masu fama da ciwon sukarin, hukumar ta ce ya kamata a tashi tsaye wajen koya wa masu dauke da cutar yadda zasu yi rayuwarsu ta yau da kullum.

Sannan kuma a bada himma wajen wayar wa jama'a kai game da matakan rigakafin cutar.

Shirin mu kenan na wannan makon. A yi sauraro lafiya.