Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Rikicin manoma da makiyaya

Image caption An dade ana samun rikici tsakanin manoma da makiyaya

An dade ana fuskantar rashin jituwa tsakanin manoma da makiyaya, inda manoman kan zargi makiyaya da kora dabbobi cikin gonakinsu suna yi masu barna.

Wannan lamarin da kan haddasa tashin hankali a wasu kasashen Afrika.

A Najeriya, yanzu haka an tsaurara matakan tsaro a wasu yankuna a jihohin Nasarawa da kuma Benue sakamakon wata rigima tsakanin fulani makiyaya da 'yan kalibar Tibi, da suka zargin fulanin da barnatar masu da amfanin gona.

Kusan a duk shekara sai an samu rohotannin tashin hankali tsakanin makiyaya da manoma akan zargin kora dabbobi cikin gonaki.

To domin tattaunawa akan bazuwar wannan matsalar da kuma yadda za'a magance ta mun gayyato:

1. Shu'aibu Habu Sri-Lanka maigana da yawun manoma a karamar hukumar Yamaltu Deba, a Jihar Gomben Najeria wanda kuma ya ce kwananan, shanun wasu fulani sun cinye masa anfanin gona.

Akwai kuma Saleh Bayeri Sakataren Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyatti Allah a Najeriya, da Peter Idocer Kwembe shugaban matasa 'yan kabilar Tibi mazauna jihar Nasarawa a Nigeria.

Sai kuma ASP Abubakar Muhammad jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yansanda a jihar Katsina kuma mamba a wani kwmaitin da gwmantin jihar ta katsaina kafa don shawo kan rikici tsakanin makiyaya da manonma 07059011309

Sai kuma masu sauraron mu da za mu ji ra'ayoyinku akan wanna batu imma ta waya kai tsaye.