Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Janye tallafin man fetur a Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zangar adawa da janye tallafin mai a Legas

Batun cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi na ci gaba da janyo kace-nace a dukkan sassan kasar, inda jama'a ke ta zanga-zanga a sassan kasar da dama.

Tun dai bayan da shugaba Goodluck Jonathan ya bada sanarwar cire tallafin man a ranar daya ga wannan watan, wato ranar da aka shiga sabuwar shekarar nan ta 2012, jama'a da dama suka kara nuna adawarsu da wannan mataki. Inda kungiyoyin kwadago da na fararen hula daban-daban a sassa da dama na kasar suka fara zanga-zangar da suka ce ba za su daina ba har sai gwamnati ta janye wannan mataki .

Najeriya dai ita ce kasa ta shidda dake da arzikin man fetur a duniya kuma a baya an sha daukar matakan kari a farashin man ba tare da ganin wani sauyi a rayuwar 'yan kasar ba, illa lokacin da Marigayi Janar Sani Abacha ya kafa Hukumar sarrafa rarar man Fetur ta PTF.

Ko da ya ke a wannan karon ma gwamnatin na cewa kudaden da za a samu, bayan an cire tallafin, za a yi amfani da su ne wajen inganta rayuwar talakawan.

Sai dai masu sukar janye tallafin na cewar, dodo-rido ake yiwa 'yan Najeriya, kuma sun gaji da gafara-sa-ba su ga kaho ba, saboda akwai wasu ababuwa na almubazzaranci da kudade da Gwamnatin ke yi da ya kamata ta daina .

Gwamnatin dai ta bugi kirji ta kuma janye tallafin man, abinda kuma tuni ya fara shafar rayuwar miliyoyin jama'a a Najeriyar, da ma wasu kasashe dake makwabtaka da ita.

To ko ta yaya cire tallafin man fetur din ya ke shafar rayuwarku? Kuma ta yaya kuke ganin za'a shawo kan wannan takaddama? Kadan kenan daga cikin abubuwan da za mu tattauna a kai a Filin mu na Ra'ayi Riga na wannan makon.