Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Hadin kan Musulmi da Kirista a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An sha fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da addini a Najeriya

Rohotanni daga jihar Kano a Arewacin Najeriya na cewa wasu abubuwa da ake zaton bama-bamai ne sun tashi a sassa daban - daban na birnin.

Cikin wuraren da aka samu fashewar, har da ofishin mataimakin babban sufeton 'yan sandan kasar, da kuma wasu ofisoshin 'yan sanda a sassa daban daban na birnin.

Tuni dai yanzu haka aka kafa dokar hana fita sam sam a garin sakamakon wannan abu, kuma Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai wadannan jerin hare haren, ta na mai cewar ta kai harin ne saboda watsin da aka yi da bukatar ta ta neman a sako 'yan kungiyar da ake tsare da su.

A shirin mu na Ra'ayi Riga na wannan makon, mun duba wannan batun na hare-hare a Kano da kuma lamarin yajin aiki da zanga-zangar da aka rika yi a kwanan nan a Najeriya, na neman tilastawa gwamnati ta maido da tallafin man da ta janye.

Inda Musulmi da Krista suka zama tsintsiya madaurinki daya a gwagwarmayar.

Wannan hadin kai, har ya sa kowane bangare yana kare dan uwansa a lokacin ibada.

Alhali tun kamin wannan lokacin, matsalar tsaro ta sa wasu sun fara kaura suna komawa yankunansu na asali, sakamakon irin barazana da kuma hare-haren da kungiyoyi irinsu Boko Haram ke kaiwa, wadanda suka janyo asarar rayuka da yawa.

To ganin cewa an dan sami ci gaba a kyautatuwar dangantaka tsakanin manyan addinan biyu a Najeriyar, ko wadanne matakai ne ya kamata a dauka don ganin ba a koma gidan jiya ba?

Bakin da muka gayyato a shirin - baya ga masu sauraro da ke kan layi - sun hada da:

Sheikh Dr Khalid Aliyu Abubakar, Sakatare Janar na kungiyar JNI (Jama'atu ...) da Rev Matthew Kuka, Bishop din cocin Roman Katolika a Sakkwato.

Da Dr Sadiq Isa Radda, malami a sashen nazarin zamantakewar dan adam, a jami'ar Bayero da ke Kano.