Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Shin akwai bukatar guguwar sauyi a Afrika?

Image caption Jama'a da dama na nuna adawarsu da gwamnatoci da dama a Afrika

A daidai lokacin da ake bukukuwan tunawa da boren da aka yi a kasashen Tunisia da Masar wanda ya kifar da gwamnatocin kasar, sannan ya haifar da bore a wasu kasashen Larabawa: Tambayar ita ce ko za a sami makamancin wannan boren a kasashen Afrika?

An kifar da gwamnatoci, masu mulkin kama-karya sun sha kasa, an watsa boren a gidajen talabijin ta hanyar da ba a taba tsammani ba watanni 12 da suka gabata.

Nahiyar Afrika na daga cikin sassan duniya da ke da shugabannin da suka dade suna mulkin kama-karya - kuma wannan shi ne abinda mazauna kasashen Larabawan ke adawa da shi.

Tun daga lokacin, jama'a a wasu kasashen Afrika Kudu da sahara sun yi ta fatan samun irin wannan sauyi a kasashensu.

Shin ko kuna ganin akwai bukatar wata guguwar sauyin a irin wadannan kasashen na kudu da sahara? Ta yaya za a karfafa demokradiyya a Afrika? Wasu ke nan daga cikin abubuwan da muka tattauna a shirinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon.