Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shin akwai 'yan maula a birnin Landon

Image caption Birnin London na daga cikin manyan birane a duniya

A filin Taba Kidi Taba karatu na wannan makon, munn tattauna kan yadda ake samun masu maula a birnin Landon, da kuma yadda wani barawo ya yi amfani da cincin a matsayin bam domin yin sata.

Za kuma muji yadda hukumomi a kasar Indonesia suka yanke shawarar biyan mazaje albashinsu ta asusun matansu.

An dauki wannan matakin ne bayan da matan suka yi korafin cewa mazan na danne musu hakkinsu ta hanyar amfani da kudaden ta hanyar da bata dace ba.

Matan sun kuma zargi mazajen na su da basu kudin abinci kacal, yayin da suke ficewa domin daukar nauyin wasu matan a waje.