Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Samar da tsaftataccen ruwa ga jama'a

Image caption Mutane da dama na fama da karancin ruwa musamman a yankunan karkara

Shekara ta 2015, ita ce wa'adin da majalisar dinkin duniya ta dibarwa kasashe na cimma wasu muradu - irinsu rage talauci, da kyautata ilimi, da samar da ruwan sha, da tsabtace muhalli da dai sauransu.

Amma tun ma kamin cikar wa'adin, a wannan makon ne majalisar ta fitar da rahoto, inda ta ce an cimma muradin samar da tsabtataccen ruwan sha, inda a yanzu kashi tamanin da tara cikin dari (89) na al'ummar duniya suna samun ruwan sha mai tsabta, kashi 76 cikin dari a shekara ta 1990.

Sai dai har yanzu kusan mutane miliyan 800 ne ke shan ruwa maras tsabta a duniya, kuma kashi arba'in cikin dari suna zaune ne a yankin Afirka na kudu da hamadar Sahara.

Rashin tsabtar muhalli shine ya fi zama kalubale daga cikin sauran muradun karnin da ba a cika ba - musamman a kasar Indiya, inda fiye da rabin al'ummar kasar - watau miliyan dari shidda da ashirin da shidda (626) - ba su da makewayi.

Filin Ra'ayi Riga na wannan makon zai tattauna ne akan batun samar da ruwan sha da kuma tsabtar muhalli a yankunan da kuke, da kuma duba ko za a iya cika muradun karnin nan da shekaru uku masu zuwa.

Baya ga masu sauraro da ke kan layi, mun kuma gayyato bakin da suka hada da Hon Alhassan Ado Doguwa, shugaban kwamiti mai kula da muradun karni a majalisar wakilan Najeriya.

Da Alhaji Abubakar Gege, shugaban hukumar RUWASSA, mai kula da samar da ruwan sha da kuma tsabtar muhalli a yankunan karkara, a jahar Katsina.

Sai kuma Malam Sidik Ali, shugaban kungiyar 'yan jaridu ta Nijar, mai kula da samar da ruwan sha.