Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra’ayi Riga: ‘Mata na fuskantar kalubale a Najeriya’

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mata dai sunfi maza yawa a Najeriya

Hukumar Raya Al'adu ta Burtaniya, wato British Council ta ce mata a Najeriya sun fi fuskantar kalubalen rayuwa fiye da maza, kuma lamarin ya fi kamari a yankin Arewacin kasar idan aka kwatanta da yankin kudu.

Rahoton dai ya nuna cewa, yawan al'ummar Najeriya ya kai miliyan 162 da rabi, kuma fiye da miliyan tamanin daga cikinsu mata ne.

Sai dai duk da cewa matan sun kai kashi 49 cikin dari na jama'ar Najeriyar, an bar su a baya a fannonin rayuwa da dama, kamar su ilimi, kiwon lafiya, talauci, siyasa da makamantansu.

Rahoton ya kuma ce, dole ne a yi la'akari da matan a duk wasu shirye-shirye da za a yi a kasar, idan har ana son makomar kasar ta kasance mai kyau.

Barin matan a cikin kuncin rayuwa in ji rahoton ka iya shafar makomar Najeriyar baki daya. To ko ina ma fita daga wannan hali?

Wadannan sune batutuwan da za mu tattauna akai a filin Ra'ayi Riga na wannan makon.

Inda muka gayyato bakin da suka hada da:

Hajiya Zainab Maina, Minista mai kula da harkokin mata a Najeriya, wadda a yanzu haka take Dubai. Da Hajiya Saudatu Mahdi, shugabar kungiyar WRAPA mai kare hakkin mata a Abuja.

Da kuma Alassan Doguwa, shugaban kwamitin kula da muradun karni a majalisar wakilan Najeriya.

Sai kuma shugaban Tarayyar Majalisun Afirka a kan muradun karni a jihar Kano.