Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Bunkasar tattalin arzikin nahiyar Afrika

Image caption Jama'a dai na fama da dinbin talauci a mafi yawan kasashen na Afrika

Wani rahota da kungiyar Africa Progress Panel ta fitar, ya ce wasu kasahen Afrika na samun bunkasar tattalin arziki cikin hamzari ciki kuwa har da Najeriya. To ko jama'a na gani a kasa?

Rahoton ya ce ci gaban ya dara na sauran nahiyoyi, alal misali, ci gaban da kasar Ethiopia ta samu daga 2005 zuwa 2009 ta fuskar tattalin arziki yafi na Kasar China.

A kasar Ethiopia din ne kuma shugabannin Afrika da sauran masu fada aji a harkar kasuwanci a duniya ke kammala wani taro a ranar Juma'a a kan tallata damar da ake iya samu a Afrika ta fuskar kasuwanci da tattalin arziki da samar da aikin yi da kyautata shugabanci na gari da kuma inganta muhalli.

Wadanda suka shirya taron sun ce shida daga cikin kasashe 10 dake samun bunkasar tattalin arziki cikin sauri a duniya na a Afrika ne ciki kuwa har da Najeriya.

Sai dai duk da haka wasu da dama a Afrika na cewa ba sa gani a kasa.

To ko yaya batun yake a zahiri? Wacce irin dama ce ake da ita a Afrika din? Wasu kenan daga cikin abubuwan da zamu tattauna akai a filin na wannan makon.

Domin tattaunawa kan wannan batu mun gayyato wasu baki wadanda suka hada da:

Dr Husaini Abdu, shugaban kungiyar ACTIONAID a Najeriya mai yaki da talauci.

Da Malam Kabiru Sa'idu Sufi malami a makarantar sharar fagen shiga Jami'a a Kano kuma mai sharhi a kan al'amurran yau da kullum.

Muna kuma tare da Alhaji Alhassan Abdullahi wani dan jarida a kasar Ghana.