Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: karuwar masu cutar hawan jini a duniya

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Cutar ta fi karuwa a nahiyar Afrika a cewar rahoton na WHO

Wata kiddiga da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fitar, ta nuna cewa jinin kowanne daya daga cikin mutane ukku a duniya yana hawa.

Rahoton yace yanzu ana samun karuwar kamuwa da ciwon hawan jinin musamman ma a kasashe masu tasowa.

Yawancin masu fama da hawan jinin a kasashen Afrika dai ba su ma san suna fama da cutar ba, duk da cewa, ana iya yi musu magani.

Kuma rashin samun maganin ne ke kai ga samun shanyewar rabin jiki, da kuma sauran cututtuka da suka shafi zuciya.

Rahoton na WHO ya kuma ce, a jamhuriyar Nijar kashi hamsin cikin dari na maza baligai na fama da hawan jini, yayin da kasashen Malawi da Mozambique suka biyo bayan Nijar din a yawan masu fama da cutar.

A yawancin kasashe masu tasowa dai akwai karancin wuraren gwaji da kuma tsadar kiwon lafiya, kuma ana ganin hakan yana hana jama'a dake fama da hawan jini samun kulawa.

To ko yaya girman wannan matsala take a yankunan ku? Kuma me ke haddasa karuwar masu fama da hawan jinin? Kuma ta yaya za'a shawo kan lamarin?

Wadannan sune batutuwan da zamu tattauna a filin Ra'ayi Riga na wannan makon.

Kuma domin tattauna wannan batu mun gayyato bakin da suka hada da: Dr Mansur Kabir, daraktan kula da kiwon lafiyar jama'a a ma'iakatar kiwon lafiya ta Najeriya.

Sai Dr Iliyasu Idi, shugaban kungiyar kwararrun likitoci na Niger, da kuma Dr Bashir Mijinyawa, shugaban kungiyar likitocin ciwon suga a Najeriya.