Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Shekara guda da hawan Jonathan mulki

Image caption Shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan

A ranar Talatar ne shugaban Najeriya Dr Goodluck Ebele Jonathan ya cika shekara guda cif cif a matsayin zababben shugaban kasar.

Ko da yake dai kafin zabensa da aka yi a watan Afrilun shekara ta 2011, Mista Jonathan ya shafe kusan shekara guda akan kujerar mulki sakamakon rasuwar tsohon shugaban kasar, Alhaji Umaru Musa 'Yaradua.

A jawabinsa na shan rantsuwar jan ragamar kasar, shugaba Jonathan ya dauki alkawarin tabbatar da hadin kan 'yan kasar tare da yin ayyukan da zasu ingantan rayuwar al'umma.

A cewarsa kuma, zai bullo da wani sabon tsarin ciyyar da Najeriya gaba wato 'Tranformation Agenda, tsarin da yace zai bi sau da kafa don ganin abubuwa sun inganta.

Har ila yau, shugaba Jonathan a jawabinnasa a ranar 29 ga watun Mayun 2011, ya dauki alkawarin samarda ingantaccen ilimi a makarantun Najeriya tare da samar da abubuwan kiwon lafiya.

Har ma da bada fifiko akan ayyukan noma don abinci ya yawalta sannan a samarda da ayyukanyi a tsakanin 'yan kasar.

Bugu da kari kuma ya sha alwashin samar da isasshen wutan lantarki a Najeriya don bunkasa cigaban tattalin arzikin kasar.

Yanzu dai shekara daya kenan da Mista Jonathan ya yiwa 'yan Najeriya wadannan alkawuran dama wasu da dama, amma tabbaya anan itace, shin ko 'yan kasar sun gamsu da kamun ludayinsa.

Shin shekara guda ya isa ace Allasan barka, ko kuwa shugaban yan bukatar karin lokaci don ya cimma burin da yasa a gaba.

Domin tattauna wannan batun, yanzu muna tare da Barrister Ahmed Ali Gulak: Mai baiwa Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan shawara ta fuskar Siyasa wanda ke ofishinmu na Abuja, da kuma Malam Nasir Ahmed El-Rufai: Jigo a Jam'iyyar Adawa ta CPC a Najeriya.

Sai kuma Dr Kabir Mato Shugaban sashin kimiyar siyasa na Jami'ar Abuja, kuma mai sharhi akan al'amuran yau da kullum wanda shima yake ofishinmu na Abuja.

Haka nan kuma ta wayar salula muna tare da wasu daga cikinku, ku, masu saurarenmu!