Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Darasi kan murabus din Paparoma

Pope Benedict
Image caption Paparoma Benedict shi ne na farko da yayi murabus cikin shekaru 600

A farkon makon nan ne Paparoroma Benedict ya bada sanarwar cewa zai yi murabus daga mukaminsa a karshen wannan watan na Fabreru.

Ya danganta batun sauka daga kan mukamin ne da tsufa da kuma rashin koshin lafiya.

Wannan batu shi ya sa aka shiga tafka muhawara game da shugabannin da kan yi wa mulki rikon mutu-ka-raba.

A 'yan shekarun da suka wuce dai an sha samun takun-saka a wasu kasashe game da koshin lafiyar shugabanni.

Irin haka ta faru a Najeriya zamanin mulkin shugaba Umaru Musa 'Yar'adua inda aka yi ta kai ruwa-rana kan ko rashin lafiyar da yake fama da ita, ta sa ya kamata yayi murabus, ko majalisar dokoki ta tsige shi, a karshe ta Allah ta kasance ya rasu a kan mulki, kafin a rantsar da mataimakinsa Goodluck Jonathan a matsayin shugaban kasa.

Yanzu haka a 'yan kwanakin nan an yi ta jayayya game da koshin lafiyar wasu gwamnoni a Najeriyar.

Baya ga Najeriya akwai wasu kasashen da ake fuskantar irin wannan jayayyar, suna hada da Kamaru, har ma da Ghana kafin rasuwar shugaba John Atta Mills.

Shin wane darasi ya kamata shugabannin su koya daga matakin da Paparoma Benedict din ya dauka, wanda aka ce shi ne karon farko cikin shekaru kusan dari shidda?

Wannan shi ne batun da muka tattauna a filinmu na Ra'ayi Riga na wannan mako: