Ra'ayi Riga: Mutuwar Chinua Achebe

Ra'ayi Riga: Mutuwar Chinua Achebe
Chinua Achebe
Bayanan hoto,

Chinua Achebe ya shahara sosai a fagen adabin Turanci

Shahararren marubucin nan dan Najeriya Farfesa Chinua Achebe ya rasu a Amurka yana da shekaru 82 da haihuwa.

An haifi Chinua Achebe a shekarar 1930 - inda kuma ake masa lakabi da uwa-uba a fannin adabi a anahiyar Afrika.

Littafinsa na farko - 'Things Fall Apart' wanda aka wallafa a shekara ta 1958 - ya mayar da hankali kan tasirin mulkin mallaka ga al'ummar Afrika; yana nuna yadda aka nakasta al'adu da halayyar gargajiya ta mutane.

Tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela, ya ce kasancewar da yayi tare da litattafan Chinua Achebe, ya debe masa kewar gidan yari lokacin ake tsare da shi.

Da dama daga cikin wadanda suka karanta rubuce-rubucensa, sun tabatar da hakan - musamman yadda labaran suke ratsa mutane.

Kasa da shekaru goma, itama Najeriyar da kanta sai ta fara tangal-tangal: Kabilar Chinua Achebe, ta Igbo, sun nemi ballewa daga Najeriya - dalilin da yasa kasar ta fada yakin basasa na shekara uku.