Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yunkurin ceto Arewacin Najeriya'

A karshen shekarar da ta gabata ne aka kaddamar da wani dandali a gidan adana kayan tarihi na Arewa House dake Kaduna, Najeriya.

An bude dandalin ne da nufin tunkarar wasu matsaloli da suka addabi arewacin Nijeriya da nufin nemawa yankin mafita.

Dr Usman Bugaje, daya daga cikin wadanda suka jagoranci taron da aka yi na kaddamar da dandalin ya kawo mana ziyara sashen Hausa na BBC, kuma Ahmad Abba Abdullahi ya tattauna da shi domin jin karin bayani kan yunkurin nasu: