Nakasa da Shugabanci a Najeriya

Nakasassu a Najeria

A shirin Ra'ayi Riga na wannan mako mun duba irin rawar da ya kamata a ce Nakasassu na takawa a tsarin mulkin Demokuradiya a Najeriya . Domin haka ne muka shirya wata tattaunawa ta musamman a Lafiya, Jihar Nasarawa, inda Gwamnan Jihar Alhaji Tanko Al-Makura da wasu jama'a suka shiga cikin shirin.