Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi riga: Tattalin arzikin Najeriya

Ziyarar da Christine Lagarde, shugabar asusun bada lamuni ta duniya ta kawo Nigeria, ta taso da batutuwa da dama game da yanayin da tattalin arzikin kasar yake ciki. Nijeriya dai kasa ce wadda jigon tattalin arzikinta ya dogara a kan albarkatun mai fetur wanda yanzu farashin sa ya fadi kasa warwas a kasuwannin duniya.