An soma rubibin mota mai aiki da lantarki

Image caption Sabuwar motar Tesla mai amfani da lantarki za a soma sayar da ita ne a karshen shekara ta 2017

Shugaban kamfanin kera motoci na Tesla, Elon Musk ya ce yawan odar da kamfanin ya samu na motorsu mai amfani da lantarki ta kai kimanin 276,000.

Kamfanin mai shalkwata a California ya gabatar da motar ne mai daukar mutane biyar kuma ita ce mafi karancin kudi a jerin motocin da kamfanin ke kerawa, wacce kuma ba ta amfani da mai.

Sai dai a cewar Mista Musk, ba lalle ba ne yawan motocin da aka yi odar ya kai yawan wadanda za a sayar idan aka soma sayar da ita a kasuwa a karshen 2017.

Masu sha'awar motar na iya yin odar ta kafin a soma sayar da ita a kasashe da dama ciki har da Britaniya da yankin Ireland, da Brazil da India da China da kuma New Zealand, sai dai ana bukatar masu son mallakar motar da su biya dala 1,000 a matsayin kudin ajiya.

Mista Musk ya ce burin kamfanin shi ne ya kera kimanin motoci 500,000 a shekara idan ya soma aiki gadan-gadan.

Farashin motar mafi karanci zai soma ne daga dala dubu 35, kimanin sama da naira miliyan 6, kuma motar za ta yi tafiyar kimanin mil 215 watau kilomita 346 kafin a yi mata caji.