Matsalar fatara a Najeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Kuncin rayuwa a Najeriya

Nigeria, kamar sauran wasu kasashe makwabtanta, kuncin rayuwar da jama'a ke fama da shi a sakamakon matsalar tattalin arziki, matsala ce da kusan ta zama tsumagiyar kan hanya - fyadi yaro - fyadi - babba, dama sassa da dama na wasu kasashen Afrika. To shin ya matsalar take a yankunanku? Kuma wadanne matakai ne ya kamata gwamnatoci su dauka domin saukaka ma jama'a halin da suka shiga? Wasu kenan daga cikin batutuwan da muke tattaunawa kenan a filinmu na Ra'ayi Riga.