Zakarun Firimiya na Ingila
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi:Leicester ta yi ba-zata a Firimiya

Yayinda aka kammala gasar Firimiya ta bana a nan Ingila, kulob din Leicester City ne yayi ba-zata na lashe kofin gasar. Inda ya ba marada kunya, ya sha gaban manyan kulob kulob irin su Chelsea, da Arsenal da Mancher United da kuma Mancher City da sauran su. Me kuke jin ya taimaka wajen nasarar da kulob din na Leicester City ya samu? Wane darasi za a koya, me kuma za a yi a inganta gasar Primiya ta kasashen Afrika irinsu Nigeria? Wasu kenan daga cikin batutuwan da zamu tattauna a Ra'ayi Riga.