An gwabza fada tsakanin 'yan Boko Haram ya junansu

Abdou shugaba Yakubu G.
Bayanan hoto,

Abdou Halilou da Tsohon shugaban Najeriya Yakubu Gawon

Rahotanni daga Najeriya na cewa an yi arangama tsakanin bangarori biyu na kungiyar Boko Haram.

Rikicin dai ya samo asali ne tun bayan da kungiyar IS mai ikirarin kafa daular Musulunci ta sanar da Abu Mus'ab Al-Barnawi a matsayin sabon shugaban kungiyar ta Boko Haram, wacce ta kira resehnta na yammacin Afirka.

Rashin jituwar ya kara ta'azzara ne a makonni biyu da suka gabata, lokacin da bangaren Al-Barnawi ya kai hari a kan mabiya Abubakar Shekau.

Kawo yanzu dai ba a iya tantance irin abin da rigimar tsakanin bangarorin kungiyar biyu ta haddasa ba sakamakon rashin kyawun hanyoyin sadarwa na zamani a arewa maso gabashin kasar.

Bambancin akida ne ya kawo rabuwar-kai a tsakanin bangarorin biyu.

Bangaren Al-Barnawi dai na zargin mabiya Abubakar Shekau da tsananta hare-hare a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Shi kuma Shekau yana zargin bangaren Al-Barnawi da cin amanar kungiyar.

Wasu dai na yi wa rigimar da ta dabaibaye Boko Haram kallon wata dama ga hukumomin tsaro su karasa murkushe 'ya'yan kungiyar.