Wasu 'yan Brazil sun yi wa shugaba Michel Termer ihu

Mista Temer da matarsa na cikin manyan bakin da suka halarci bikin bude gasar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Temer ya zama shugaban Brazil ne bayan an tsige Dilma Rousseff

An yi wa shugaban kasar Brazil, Michel Temer ihu a yayin da ake bude wasan Paralympic a Rio de Janeiro.

Dubban mutane ne suka hallarci bikin bude gasar daga kasashen duniya daban-daban, inda aka shafe awa biyu ana yi a filin wasa na Maracana.

A ranar Alhamis ne dai za fara gasar kuma ana sa ran Dame Sarah Storey, 'yar Birtaniya za ta zama macen da za ta fi yin fice a gasar.

A lokacin bikin bude wasan, Carlos Martin, wanda hannunsa na dama ba ya aiki kwata-kwata, ya rera taken kasar Brazil da na'urar Piano.