Vladimir Putin ya fi Obama karɓuwa a wajen 'yan kasarsa

Donald Trump

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Donald Trump ya ce idan ya ci zabe zai yi aiki tare da Putin

Dan takarar neman shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump ya ce shugaban Russia, Vladimir Putin, ya fi Barack Obama saboda ikon da yake da shi a kan 'yan kasarsa.

Trump ya bayyana hakan ne a lokacin mahawarar da suka yi da abokiyar takararsa, Hillary Clinton, a New York, ranar Laraba.

Mista Trump ya fada wa masu bibiyar mahawar tasu cewa shugaban Russia, Vlamidir Putin na kaso 82 na goyon bayan 'yan kasarsa.

Ya kara da cewa idan aka zabe shi a matsayin shugaban Amurka "zai yi aiki tare da Putin."

Wannan dai ya zo ne a ranar da babban jami'in hukumar tsaron Amurka ya zargi Russia da dasa danba na rashin zaman lafiya a duniya.