Kotu a India ta yanke hukuncin kisa kan watsa guba,

Mazaje na tirsasa wa mata a Indiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An sha samun afkuwar hare-haren guba kan mata a Indiya

Wata kotu a birnin Mumbai na India ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa sakamakon zuba wa wata mata sinadarin Acid a jiki.

Ankur Panwar dai ya sheka wa Preeti Rathi sinadarin ne a wata tashar jirgin kasa mai yawan hada-hada, shekaru uku da su ka gabata.

Preeti Rathi, mai shekara 23, ta gamu da kaddarar ne jim kadan bayan saukar ta a birnin na Mumbai da nufin shiga aikin sojan ruwa.

Kuma bayan wata daya da faruwar al'amarin ne Preeti Rathi ta mutu.

Sai dai kuma Ankur ya ce ya yi aika-aikar ne saboda marigayiyar taki amincewa ta aure shi.

Mahaifinta, wanda yake magana bayan fitowa daga kotu, ya ce kotu ta yi adalci.