Barack Obama ya ce Trump 'sakarai' ne

Zuwan Barack Obama Laos

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Barack Obama ya ce shugabancin Amurka bai kamaci 'sakarai'.

Shugaban Amurka, Barack Obama ya ce dantakarar neman shugabancin Amurkar a jam'iyyar Republican, Donald Trump 'shasha ne'.

A ranar Laraba ne dai Donald Trump ya ce shugaban Russia, Vladimir Putin ya fi Obama iya mulki, a saboda haka ya fi shi karbuwa a wurin 'yan kasarsa.

Hakan ne ya har zuka Obama mayar da martani, a inda ya bayyana Trump da 'shashasha' wanda bai san inda duniya ta sa gaba ba.

Obama dai wanda ya mayar da martanin a lokacin da yake magana a Laos na kasar Philippines, ya ce kujerar shugabancin Amurka ba ta dace da Donald Trump ba.