Apple ya yi wayoyin da suka banbanta da iphone 6

Asalin hoton, Reuters
Apple ya fito da iphone 7 da iphone 7plus
Kamfanin Apple mai yin wayar salula samfurin iphone ya kaddamar da sabbin wayoyin iphone 7 da iphone 7plus.
Kowacce shekara dai kamfanin na Apple yana fito da samfurin iphone sabo da ke zuwa da sabon fasali da kuma sabuwar manhaja.
Babban abin da ya banbanta iphone 7plus da wayar da ta gabace ta wato iphone 6, shi ne batir.
Batirin wayar yana da kwari da juriya sannan kuma ya dara na iphone 6 rike caji da awa biyu.
Sannan kuma wayar ta iphone 7plus za ta iya yin minti 30 a cikin ruwa ba tare da ta yi komai ba.
Wani karin banbanci tsakanin wayoyin shi ne girman fuska wato 'screen' abin da ya sa ita iphone 7plus take da kamarar daukar hoto har guda biyu.
Apple dai na gogayya ne da Samsung a harkar wayoyin salula da suka fi kasuwa a duniya.