Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allawadai da Koriya ta Arewa

Ban Ki-moon
Bayanan hoto,

Ban Ki-moon ya ce gwajin makamin nukiyan karen tsaye ga kudirin da kwamitin tsaro na Majalisar ta zartar

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allawadai da gwajin makamin nukiliya karo na biyu da kasar Koriya ta Arewa ta yi.

Babban Sakataren Majalisar, Ban Ki-moon ya bayyana matakin a matsayin karen tsaye ga kudirin da kwamitin tsaro na Majalisar ya zartar.

Gwajin shi ne mafi girma da kasar ta taba yi.

Shugaba Obama ya bayyana lamarin a matsayin babban barazana ga tsaron yankin dama duniya baki daya.

Anata bangaren kasar Koriya ta Kudu ta zargi shugaba Kim Jong-un a matsayin wani da bashi da hankali, yayin da Rasha ta ce gwajin wani babban kasada ce.

Ma'aikatar kasashen waje ta China ta ce shugabannin kasar ba su ji dadin gwajin makamin ba, a inda suka ja hankalin Koriya ta Arewa da ta guji cigaba da gwaje-gwajen.

Ita dai Kasar Korea ta Arewa ta ce ta samu nasarar yin wani gwajin makamin nukiliya karo na biyu, a cigaba da bujire wa dokokin Majalisar Duniya.