Mourinho ya firgita da Manchester City

Mourinho yana fargabar rashin wasan Aguero

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Jose Mourinho ya ce yana tsoron abin Man City za ta yi

Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya ce rashin Sergio Aguero a Manchester City zai sa samun nasara a kan kulob din ya yi wuya.

A ranar Asabar ne dai za a fafata tsakanin Manchester United da Manchester City, a mako na uku na gasar Premier bana.

Dan wasan, dan kasar Argentina, mai shekara 28, ba zai buga wasanni uku ba sakamakon hukuncin da hukumar FA ta yi masa kan yi wa dan wasan West Ham gula.

Aguero dai ya zura kwallaye uku a kakar wasannin Premier bana.

Sai dai kuma kocin Manchester United, Jose Mourinho ya ce rashin Aguero zai haifar da kasa gane inda Man City ta dosa.

Ya ce " Ba zai yi wasa ba amma za su bayar da mamaki."

Ya kara da cewa "idan Aguero yana wasa, mun san tsarin wasan."

Mourinho yana fargabar cewa Kelechi Iheanacho ko Raheem Sterling ko kuma David Silva ka iya yin basaja a matsayin lamba tara.