Nigeria za ta inganta kiwon zuma domin rage dogaro da mai

Asalin hoton, Getty Images
Masu kiwon zuma a Najeriya na cigaba da samun tallafi wajen kungiyoyin bayar da agaji
A Najeriya, an gudanar da wani taro a karon farko kan yadda za a inganta noman zuma ta yadda za a rage dogaro da man fetur.
Taron dai wanda kungiyar tarayyar Afirka da ma'aikatar aikin gona ta Najeriya da wasu manyan kungiyoyi na duniya irinsu hukumar bayar da agaji ta USAID suka hada, ya tattauna kan kalubalen da masana da masu noman zuma ke fuskanta da kuma yadda za shawo kasnu.
Malam Ya'u Sarkin Baki, shi ne shugaban kungiyar masu noman zuma a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya.
Mallam Ya'u ya ce manufar shirin shi ne horar da jami'an zuma na zamani, domin su koyawa mutanen jihohinsu na aikin zuma na zamani da nufin samar da isashiyar zuma da zasu ishi Afirka dama kasashen Turai.
Ya'u ya kara da cewa a Najeriya, masu kiwon zuma na fuskantar kalubale dama saboda rashin samun horo akan yadda aka kiwon zuma.