Ɗalibai mata na da ikon su sa Hijabi a Kenya

Makarantun gwamnati a Kenya
Bayanan hoto,

Tun da farko makarantun gwamnati a Kenya sun yarda da 'yan mata su rinka sa hijabi a makarantun

Wata kotun daukaka kara a Kenya ta ce dalibai mata musulmai a Kenya za su iya sanya hijabi a matsayin kayan makaranta.

Hukuncin kotun dai ya biyo bayan karar da wata coci ta shigar tana kalubalantar sanya hijabin da 'yan makaranta mata ke yi a makarantun da su ke karkashinta.

Wata makarantar kiristoci dai a kasar ta haramtawa 'yan mata musulmai sanya hijabi da wando.

Cocin ta bayar da dalilin hana Musulman sanya hijabi da cewa kyale 'yan makaranta sanya kaya daban-daban na haifar da gaba da rashin amincewa da juna.

Kuma wata babbar kotun kasar ta mara wa cocin baya, a inda ta ce dalibai mata musulmai bai kamata su sanya hijabi ba.

Amma kuma kotun daukaka karar ta ce ya kamata idan dai har ana son karfafa wa mutane gwiwa su yi karatu, to ya kamata a daina nuna banbanci.

Alkalan kotun sun kara da cewa tufafin addini ba daya suke da kayan ado na zamani ba.

Daman dai makarantun gwamnati sun yarda da 'yan mata su rinka sa hijabi a makarantun.

Karin bayani

Irin wannan turka-turkar dai ta faru a jihar Osun da ke kudancin Najeriya.

Makarantun dai sun hana mata musulmai sanya hijabi su shiga azuzuwa domin daukar darasi.

Hakan ne ya sa musulmin jihar suka daukaka kara, a inda kuma su ka samu nasara.

Sai dai kuma bayan nan wasu kiristoci su ma sun umarci 'ya'yansu da su rinka sanya tufafin fada-fada zuwa makarantar.

Hijabi a Turai

Batun sanya hijabi walau ko a makaranta ko kuma a gari, ya dade yana tayar da kura a kasashen duniya musamman na nahiyar Turai.

Faransa na daya daga cikin kasashen da suka hana mata musulmai sanya hijabi, bisa dalilan tsaro.

An so a yi irin wannan hukunci a kasar Turkiyya ma wadda take da yawan musulmai.

A baya-bayan nan ne kuma a Scotland aka amince wa mata musulmai 'yan sanda sanya hijabi.