A baya ma, kasar Spaniya ta sha fama da hatsarin jirgin kasa

Asalin hoton, AFP
Kasar Spaniya ta sha fama da hatsarin jirgin kasa a baya
Spain: Mutane da dama sun mutu a hatsarin jirgin kasa
Akalla mutum hudu ne suka rasa rayukansu kuma wasu mutum 49 suka jikkata a wani hatsarin jirgin kasa a kusa da garin O Porrino da ke arewa maso yammacin kasar Spaniya.
Kusan mutum 60 ne a cikin jirgin na kasar Portugal a lokacin da ya kauce daga kan layin dogo a kusa da tashar da ke garin.
Matukin jirgin kasan na cikin wadanda suka rasa rayukansu.
Daya daga cikin taragon jirgin ya katse kuma ya bar kan layin dogon yayin da ragowar kuma suka fice kadan daga kan layin dogon.
Masu aikin ceto sun garzaya wajen da hatsarin ya afkwu.
A shekarar 2013 ne dai kasar Spaniya ta yi fama da hatsarin jirgin kasa mafi muni.