Syria: Amurka da Rasha sun cimma yarjejeniya

Syria, Russia, US

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Amurka da Rasha suna da saɓani a kan rikicin Syria

Amurka da Rasha sun bayyana wani sabon shiri na kawo karshen yakin Syria da kuma soma aiwatar da shirin sasantawa a siyasance.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya ce, wannan shirin yana da ma'ana, kuma yafi duk wadanda aka yi a baya.

Ya kuma ce, idan dukkan bangarorin suka aiwatar da shi to za a samu damar tattaunawa domin samo sabuwar alkibla ga Syria.

Shirin dai ya kunshi tsagaita wuta daga lokacin da rana zata fito ranar 12 ga wannan watan.

An kuma tanadi cewa, gwamnatin Syria ta daina kai hare-hare ta sama domin kare abinda John Kerry ya kira, 'yan tawaye na gaskiya.