Syria: Amurka da Russia suna son shawo kan rikicin Syria

An kwashe kimanin shekera biyu ana gwabza fada a Syria

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Shugabannin Amurka da na Russia suna sulhu kan Syria

Amurka da Rasha sun bayyana wani sabon shiri na kawo karshen yakin Syria da kuma soma aiwatar da shirin sasantawa a siyasance.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya ce wannan shirin yana da ma'ana, kuma yafi duk wadanda aka yi a baya.

Ya kuma ce idan dukkan bangarorin suka aiwatar da shi to za a samu damar tattaunawa domin samo sabuwar alkibla ga Syria.

Shirin dai ya kunshi tsagaita wuta daga lokacin da rana za ta fito ranar 12 ga wannan watan.

An kuma tanadi cewa, gwamnatin Syria ta daina kai hare-hare ta sama domin kare mutanen da John Kerry ya kira 'yan tawaye na gaskiya'.