South Sudan: MDD ta samu Salva Kiir da laifin yaƙi

Riek Machar ne mataimakin Salva Kiir

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Salva Kiir yana zargin Riek Machar da juyin mulki

Wani sakayayyen rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ya zargi shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu da alhakin mutuwar daruruwan mutane.

Rahoton dai ya ce Salva Kiir ya bayar da umarni ne a yakin da aka gwabza a Juba, babban birnin kasar, a watan Yuli, ta hannun babban hafsan sojinsa.

Yakin kuma ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane, a kasar.

Tun dai 2013 ake yakin basasa a kasar, sakamakon rashin jituwa tsakanin shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar.

Shi dai Salva Kiir ya zargi Riek Machar da wasu mutane goma kan kokarin kifar da gwamnatinsa.