'Yan Najeriya 10 sun mutu a Makka kafin aikin hajji

'Yan Najeriya na daga cikin wadanda suka fi yawa a aikin hajji
'Yan Najeriya 10 sun mutu a birnin Makka na kasar Saudiyya, sakamakon rashin lafiya.
Shugaban Hukumara alhazai ta Najeriya, Alhaji Abdullahi Mukhtar wanda ya tabbatar wa da BBC hakan ya ce mutanen sun mutu ne sanadiyyar cututtuka iri daban-daban.
'Yan Najeriya 10 sun mutu a Saudiyya
Wannan dai na zuwa ne 'yan kwanaki kafin fara aiki hajji.
Kusan dai duk shekara sai 'yan Najeriya sun mutu a birnin mai tsarki.
Najeriya na daga cikin kasashen da ke a adadin mahajjata mafi yawa da ke kasar ta Saudiyya domin aikin hajjin.
Da daren Juma'a ne dubban mahajjatan suka fara turuwa zuwa sansanin Mina da ke wajen birnin na Makka domin halartar filin Arafa.
A ranar Lahadi mahajjatan za su yi tsayuwar arfa wadda ita ce kololuwar aikin Hajjin.