Nigeria: APC ce silar ɗage zaben Edo –– PDP

INEC ta musanta cewa an hada baki da ita.

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa dage zaben wani nau'in magudin zabe ne

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP ta zargi jami'yyar APC mai mulki da hada baki da hukumomin tsaro wajen ɗage zaben gwamnan jihar Edo da aka shirya ranar Asabar.

A cikin makonan ne dai hukumar zaben kasar ta sanar da dage zaben zuwa ranar 28 ga watan Satumba.

Hakan dai ya biyo bayan shawarar da rundunar 'yan sandar kasar da Hukumar Jami'an Tsaron Ciki, DSS suka bai wa hukumar shawarar ɗage zaɓen bisa dalilai na tsaro.

Sakataren yaɗa labarai na reshen jam'iyyar PDP a jihar Edo, mista Chris, ya ce Hukumar Zaben Najeriya ta hada baki da jam'iyyar APC.

Sai dai kuma Hukumar zaben ta musanta zargin cewa hada baki ne aka yi domin daga zaben.