An samu girgizar kasa a Tanzania

Girgizar Kasa
Bayanan hoto,

Girgizar Kasa

An samu girgizar kasa a mai karfin maki 5.7 a yankin arewa maso yammacin Tanzania, kusa da tabkin Victoria.

Masu aikin ceto sun ce akalla mutane hudu ne ake fargabar sun mutu, wasu kuma da dama sun samu raunuka inda asibitoci ke cike.

Gine gine da dama sun ruguje, inda mutane suka makale a cikinsu.

A makwaftan kasashe da suka hada da Kenya da Uganda da Rwanda da Burundi an ji alamun motsawar kasa.

Wakilin BBC a Tanzania ya ce wannan ce girgizar kasa mafi girma da aka samu a yankin cikin shekaru goma.