Nigeria: Cutar amai da gudawa ta barke a sassanin 'yan hijra

Rashin tsafta a sansanin 'yan gudun hijrar Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan gudun hijira na cikin wani hali a Najeriya

Hukomomi a Najeriya na cewa cutar amai da gudawa ta barke a sansanin 'yan gudun hijra da ke Ƙarmaji, a Abuja, babban birnin kasar.

Babban jami'i a ma'aikatar lafiya ta kasar, Dr. Sani Gwarzo, ya shaida wa BBC cewa bisa gwajin da suka aiwatar, an gano ba cutar kwalara ba ce.

Ya ce dai an samu mutanen da amai da gudawa da kuma zazzabi. Kawo yanzu dai mutane hudu ne suka kamu da cutar.

Jami'in kuma ya dangantaka barkewar cutar da rashin ruwa mai kyau da gurbataccen muhalli.