BH: 'Yan gudun hijira sun nemi mafaka a Nijar

A yanzu haka sun samu mafaka a garin Tumur

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sama da iyalai dari biyu ne suka tsere sabo da tsoron 'yan BH

Wasu sabbin `yan gudun hijira sama da iyalai 200 sun isa garin Tumur da ke kusa da Boso a jamhuriyar Nijar a yan kwanakin baya-bayan nan.

Asalinsu `yan Nijeriya da Chadi ne wadanda rikicin boko-haram da yunwa suka tilasta musu barin garuruwansu, kuma galibinsu mata ne da yara kanana.

Wasu iyalai 77 dai daga cikin 'yan gudun hijirar dai na cikin mawuyacin hali na rashin abinci da tufafi da matsugunni da kuma magunguna.

Kungiyar likitoci ta kasa da kasa Medecins Sans Frontieres ta tallafa wa mutanen da barguna, da gidan sauro da kuma kayan tsaftar muhalli.

Haka kuma kungiyar ta ba wa kananan yara abinci mai gina jiki, sannan an duba lafiyar masu hijirar a asibitin garin Tumur.

Wasu 'yan gudun hijirar sun ce sun jima suna son tserewa, amma sun kasa saboda tsoron 'yan Boko Haram.

Sun kara da cewa a yanzu sun samu damar tserewa ne sakamakon rikicin da ya barke tsakanin bangarorin kungiyar da ke adawa da juna, wadanda suke shirin gwabza fada a kusa da garinsu.