Bangladesh: Mutane 26 ne suka mutu a gobarar masana'anta

Gobara ta hallaka mutane 26 a wata masana'anta a Bangladesh

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Gobara a wata masana'anta a Bangladesh

Har yanzu jamia'n kwana-kwana a kasar Bangladesh na ta kokarin kashe gobarar da ta tashi a wani dogon ginin wata masana'anta, sa'oi 24 bayan da ta fara tashi.

Mutane akalla 26 ne suka mutu sakamakon tashin wutar a masana'antar dake Tongi arewacin Dhaka babban birnin kasar, yayinda da dama suka yi batan dabo.

Shawo kan gobarar ya gamu da cikas sakamakon wasu sinadaran da ke ajiye, da kuma robobi da ke cin wuta sosai.

Wannan shine hadarin gobara mafi muni da aka taba samu a cikin sama da shekaru uku.

Rahotannin farko sun nuna cewa fashewar wata na'urar tafasa ruwa ce ta haddasa gobarar.