Tsayuwar Arfa: Mafi muhimmancin aikin Hajji

Hajj

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mahajjata sun taru tun daga fitowar rana a filin Arfa

Aci gaba da aikin hajjin bana, kimanin mahajjata miliyan daya da rabi ne suka taru a filin Arfa a ranar Lahadin nan, wanda shi ne aiki mafi muhimmanci a aikin hajji a kasar Saudiya.

Mahajjatan sun taru ne tun daga fitowar rana a filin Arfa, yayin da suke ci gaba da gudanar da addu'o'i da karatun Al-Qur'ani mai tsarki.

A filin Arfan ne ma'aiki, Annabi Muhammad (S.A.W) ya yi hudubarsa ta karshe kafin ya bar duniya.

Aikin Hajji, daya ne daga cikin shikashikan Musulunci biyar, da ake kwadaitar da Musulmai masu hali su yi ko da sau daya ne a rayuwarsu.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Filin Arfan yana da nisan kilomita 15 daga Makkah

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

A filin Arfan, mahajjata maza na daura kyallen Irhami biyu, abin dake nuna zama cikin tsarki

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Musulmai daga ko ina a fadin duniya ne suka halarci aikin Hajjin a Saudiya

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

'Yan kasar Indonesia, kamar wannan mahaifi da yaronsa, su ne suka fi yawa a cikin mahajjatan

A ranar Asabar ne rahotanni suka ce, a karon farko cikin shekaru talatin da biyar, shugaban malamai na kasar Saudiya, Abdul Aziz al-Sheikh, ba shi ne zai gabatar da hudubar da aka saba yi kowacce shekara ba lokacin aikin Hajjin saboda rashin lafiya.

Hakan kuwa ya biyo bayan takaddamar da kalamansa suka janyo ne, lokacin da ya ce 'yan kasar Iran ba Musulmai ba ne.

Ya dai yi kalaman ne bayan shugaban addini na kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya soki yadda Saudiya ke tafiyar da shirye-shiryen aikin Hajjin.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Mahajjata na rubuta sunayensu a wurinda aka ce Annabi Muhammad (SAW) ya yi hudubarshi ta karshe

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Wasu mahajjatan na zaune, wasu a tsaye a kan dutsen Arfa suna karatun Al'qur'ani mai tsarki

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Masu aikin sa kai sun raba wa mahajjatan lema don kare rana a ranar Lahadi

Iran ta ki tura 'yan kasarta aikin Hajjin na bana, a maimakon haka, sai ta amince 'yan kasar tata su je wani aikin ibadar a birnin Karbala na Iraki ranar Asabar.

Zaman dar-dar tsakanin Saudiya da Iran ya karu bayan turmutsitsin da aka samu bara a wajen aikin Hajji a Saudiya, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2426, wadanda suka hada da Iraniyawa 464, a cewar wasu alkaluma wadanda ba na hukuma.

Saudiya da Iran din ba su da wata dangantaka ta diflomasiyya, sannan suna yawan samun sabani akan abubuwa da suka shafi yanki, wadanda suka hada da rikicin Yemen da Syria.