Mata uku sun kai hari ofishin 'yan sanda a Kenya

Attack
Bayanan hoto,

Jami'an tsaro sun killace wurin da aka kai harin

Wasu mata uku sun kai wani hari da ake zargi na 'yan bindiga ne a babban ofishin 'yan sanda na birnin Mombasa na kasar Kenya.

'Yan sanda sun ce matan sun je ofishin 'yan sandan ne domin kai rahoton sace musu wayar salula, amma sai suka daba wa 'yan sanda biyu wuka, tare kuma da jefa bom da aka hada da fetur.

An harbe harbe matan har lahira, yayin da aka wuce da 'yan sanda da suka samu raunin zuwa asibiti.

A dan tsakamin nan, ana ci gaba da samun hare hare a yankin mai teku na kasar Kenya, kuma da yawa daga cikin hare haren, kungiyar Al-Shabaab ke kai su.