Syria: Babu alamar tsagaita wuta

Mayakan kungiyar 'yan tawaye Majalisar Sojin Manbij a lardin Aleppo

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mayakan 'yan tawaye suna kokarin jan daga a Manbij, Aleppo

Yayin da ya rage 'yan sa'o'i wata yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria wadda Amurka da Rasha suka shiga tsakani aka cimma ta fara aiki, babu wata muhimmiyar alamar da ke nuna cewa fadan ya ragu.

Tun da farko a yau shugaban kasar Syrian Bashar al-Assad ya bayyana cewa gwamnatinsa ta lashi takobin kwato dukkan yakunan da ke hannun wadanda ya kira 'yan ta'adda.

Gwamnatin ta Assad dai na daukar dukkan abokan hamayyarta a matsayin 'yan ta'adda.

Da ma dai yarjejeniyar tsagaita wutar ta Amurka da Rasha ba ta dakatar da fada baki daya ba ce.

Dukkansu na da aniyar ci gaba da ragargazar 'yan kungiyar IS da kungiyoyi masu alaka da al-Ka'ida ta sama.

Sai dai kuma bambancewa tsakanin kungiyoyi masu alaka da al-Ka'ida da kuma dakarun 'yan tawaye wadanda Amurka ke marawa baya ba abu ne mai sauki ba.

Tuni dai kungiyoyin 'yan tawaye ke nuna shakku game da sassa da dama na yarjejeniyar.

Zai yi wuya wannan yarjejeniya ta kawo karshen zaman doya da manja kada'an, don haka abin da ya kamata shi ne a tantance tasirinta bisa la'akari da nasarorin da ta yi: Misali shin za a iya tabbatar da tsagaita wuta a yankunan da abin ya shafa a kuma fadada ta? Shin za a iya samun damar shiga yankunan da aka yiwa kawanya?