David Cameron zai bar Majalisar Dokokin Birtaniya

Dan majalisa David Cameron
Bayanan hoto,

A watan Yuni ne David Cameron ya sauka daga fara ministan Birtaniya

Tsohon Fira Ministan Birtaniya David Cameroon zai sauka daga mukaminsa na dan majalisar dokoki. Wannan lamari dai zai wajabta gudanar da zabaen cike-gurbi a mazabarsa ta Witney dake Oxfordshire.

Bayan zaben raba-gardamar da aka gudanar a kan ci gaba da kasancewar Birtaniya a Tarayyar Turai a watan Yuni ne dai Mista Cameron ya yi murabus daga mukamin fira minista, Theresa May kuma ta maye gurbinsa.

Da farko dai ya ce zai ci gaba da rike mukaminsa na dan majalisa har zuwa babban zabe na gaba.

Tun shekarar 2001 ne dai dan siyasar mai shekara 49 yake wakiltar mazabar Witney, a 2005 kuma ya zama jagoran jam'iyyar Conservative, sannan ya rike mukamin fira minista na tsawon shekara shida da 2010.